Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram Sama Da Talatin

Dakarun sojin hadin gwiwa na Kasarmu Nijeriya da na Kasar Chadi karkashin rundinar OPERATION ‘YANCIN TAFKI sun hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram 39 a yankin Kauwa, mayakan sojoji 20 aun samu raunuka, ana kula da lafiyarsu a asibitin sojoji.

Sojoji sun kwato makaman yaki na ‘yan ta’addan kamar haka:
a. 2 x Gun Trucks.
b. 2 x Anti Aircraft Guns.
c. 9 x AK47 Rifles.
d. 1 x HK21 Rifle.
e. 4 x Rocket Propelled Guns.

Bayan wannan nasara, shugaban sojojin Kasar Chadi Janar Tahir Erda ya ziyarci rundinar Operion ‘Yancin Tafki domin ya kara musu kaimi akan yakin da suke yi, yayi kira ga rundinar da cewa su kara bada hadin kai a tsakaninsu, sannan ya ziyarci asibitin sojoji inda ya duba lafiyar sojojin da suka samu raunuka.

Wannan sanarwan ya fito ne daga Kanar Ezindu Idimah Mataimakin mai magana da yawun sashi na 3 na rundinar Operation Lafiya Dole.

Allah Ka karawa sojoji cikakken nasara akan ‘yan ta’addan Boko Haram Amin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.