Dalilin Da Ya Sa Muka Caccaki Jonathan Akan Boko Haram Ba Ma Caccakar Buhari Akan Zamfara – Izala

 

*Mun Ci Amanar Buhari Idan Muka Ga Laifinsa Ba Mu Fada Masa Gaskiya Ba

Shugaban Kungiyar Izala na Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya amsa tambaya akan me ya sa kungiyar Izala ta rika ragargazar tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan akan rikicin Boko Haram amma yanzu ba sa yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan rikicin Zamfara? Shin kungiyar ba ta dauki bangaranci ba?

Sheikh Bala Lau ya ce duk wanda yayi wannan zargin bai musu adalci ba, domin a baya Jonathan bai ba su damar ganawa da shi ba, shi kuwa Buhari ya bude kofar ganawa da shi. Yana sauraron su sannan kuma yana daukar mataki. Don haka ba daidai ba ne Shugaban da ya bude kofar ganawa da kai sannan ka je jarida ko ka hau mumbari ka ragargaje shi.

Muna addu’ar zaman lafiya, amma hakan ba ya nufin Shugaba ya ki sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ba ne na kare rayukan ‘yan kasa da daukar matakan wanzar da zaman lafiya. Mun ci amanar Buhari idan muka ga kuskuren sa ba mu fada masa ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.