Abin Da Yasa Aka Daina Jin Duriyata – CP Wakili

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Mohammed Wakili ya ce abin da ya sa aka kwana biyu ba a ji dukriyarsa ba, ya ce yana nan “daram dam kuma muna aikinmu, a baya an rika jin duriya ta ne saboda lokacin zabe ne,” kamar yadda ya shaida wa wakilin BBC a Kano.

“Ana gwagwarmayar neman zabe, akwai abubuwa da dama wadanda na tsaro ne wanda yake dauke hankalin jama’a.”

“Saboda haka na bukatar a ji tabbaci, za a yi lafiya za a gama lafiya, wanda yake duk yanzu babu su,” inji shi.

Daga nan ya ce yana nan lafiya lau kuma yana aikinsa yadda ya kamata.

Batun shaye-shayen a jihar Kano
CP Wakili ya ce tun da aka kammala zabe zuwa yanzu sun kama ‘yan daba wadanda suke kurkuku fiye da 930.

Ya ce masu tu’ammali da miyagun kwayoyin sun sauya salo, “amma a yanzu haka muna binciken wani muhimmin batu.”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.