Za’a Ci Tarar N500,000 Ga Duk Wanda Aka Kama Da Laifin Sayen Kuri’u

 

Hukumar zabe mai cin gashin kanta ta gabatar da shawarar cin tarar wadanda aka kama da laifin sayen kuri’u Naira 500,000 ko zaman wakafi na tsawon shekaru uku, ko duk hukuncin biyu.

Hukumar zabe ta ce irin wannan hukunci shi ne zai taimaka wurin kawo karshen gurbatar harkokin zabe a Najeriya.

Babban kwamishinan hukumar na kasa mai kula da yada labarai da ilmantar da masu kada kuri’a, Mr Festus Okoye ne ya ya yi wadannan kalaman a wurin taron yakar cin hanci da rashawa a harkar zabe da ya gudana a Abuja.

Kwamishinan, wanda ya wakilci shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmud Yakubu ya yi kira ga majalisun tarayya da su kafa dokoki masu tsauri da za su hukunta masu aikatan laifukan zabe.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.