Ka Bayyana Sunayen Sarakunan Dake Da Alaka Da Barayin Shanu Ko Mu Dauki Mataki Akanka, Sakon Sarakunan Zamfara Ga Ministan Tsaro

Majalisar Sarakunan jihar Zamfara karkashin jagorancin Alhaji Attahiru Ahmad, sun ja kunnen ministan tsaro Mansur Dan Ali, kan abinda suka kira zargi da kazafi, da yayi masu na cewa sarakunan suna da hannu dumu-dumu kan harkar barayi.

Majalisar sun bukaci Mansur ‘Dan Ali da ya fito ya bayyanawa duniya sunayen sarakunan da ake zargin su da yin tarayya da barayi a jihar, Kazalika sun bayyana cewa matukar munistan tsaron bai fito ya tona asirin wadannan sarakunan ba Shakka Babu za su dauki matakin ladabtarwa, a matsayin sa na ‘Dan su.

Sun cigaba da cewa jami’an tsaro sun kasa isa inda barayin suke, kuma Boma-baman da sojoji suka jefa a wasu kauyuka kamar karamar Hukumar Gusau, da Kauyen Tangaran, da ke karamar hukumar Anka, da kuma Dumburun, a karamar hukumar Zurmi, duk ba nan ne maboyar Barayin ba.

Sannan sun kara da cewa mafi yawan wadanda aka kashe mutane ne da ba su ji ba basu ganiba, ne jami’an tsaron Sun kashe jama’a da dama, kuma wasu da dama sun jikkata, ba bisa hakki ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.