Gidauniyar Kwankwasiyya, wato ‘Kwankwansiyya Development Foundation’, za ta dauki nauyin dalibai ‘yan asalin jihar Kano da ke bukatar karo karatu a fannoni daban-daban na digiri na biyu.
A wata sanarwa da gidauniyar ta fitar, an bukaci masu bukatar samun wannan tallafin karatu da Sanata Rabiu Musa Kwankwanso zai bayar, suje babban ofishin gidauniyar da ke kan Titin Lugard, Unguwar Nassarawa, GRA, Kano.
Sharuddan samun wannan tallafin karo karatu ketare dai su ne: ya kasance dalibin ya kammala karatunsa na digirin farko da sakamakon ‘first class.’ Kuma ya kasance dalibin bai wuce shekaru 30 ba. Sannan dalibin ya zamo dan asalin jihar Kano.
Wa’adin da aka dibar wa masu sha’awar wannan tallafin na Kwankwaso ya fara ne daga yau 12/04/2019, zuwa 26/04/2019, wanda a ranar ce za a rufe karbar takardun bukatar.
Gidauniyar Kwankwasiyya Za Ta Ba Da Tallafi Ga Masu Bukatar Yin Karatun Digiri Na Biyu
