‘Yan Bindiga Sun Kwace Katsina

Gwamnan jahar Katsina Alh Aminu Bello Masari Ya shedawa Babban Sufeto ‘yan Nigeriya Muhd Adamu cewar ‘yan Bindiga sun kwace Yankuna 8 na kananan hukumomin jahar
.
A wani LABARIN kuma Sanata Mai wakiltar Gabashin jahar Taraba Sanata Emmanaul da kuma Sanata Kabiru Marafa daga jahar Zamfara sunce Kirkiro da ‘yan Sandan Jahoshi shine kadai zai kawo karshen ‘yan Bindiga dake cin Karasun Babu Babbaka a arewacin Nigeriya
.
Da yake Ganawa a Maimakon Gwamnan Mataimakin gwamnan jahar Katsina Alh Mannur Yakubu ya tabbatarwa Babban Sufeton ‘yan Sandan cewar yanzu haka ‘yan Bindigan a jahar Katsina sune suke Iko da wasu Yankuna na kananan hukumomin Jibia da Batsari da Safana da Dan Musa da Faskari da Sabuwa da Kankara da kuma Dandume, haka zalika yace akwai wasu kauyika ma’ da ‘yan ta’addar suka kwace dake yankunan Makociyar jahar zamfara
.
Mataimakin Gwamnan yace ‘yan Bindigar sun Kashe mutane da dama tare da saka Jama’a Gudun hijjira sakamakon kone musu gidaje
.
Menene ra’ayinku Gamai da wannan tashin hankulan?
.
Ya ALLAH kakawo mana karshen wannan tashin hankalin

Leave a Reply

Your email address will not be published.